Home Sabon Labari Jihar Zamfara: Majalisar dokoki ta koma ta masu kananan shekaru

Jihar Zamfara: Majalisar dokoki ta koma ta masu kananan shekaru

107
0

Daga: Abdullahi Garba jani

 

Shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara Nasiru Magarya ya ce kaso 80 cikin 100 na ‘yan majalisar dokokin jihar duk matasa ne, masu jini a jika.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya –  ya ba da rahoton cewa 4 daga cikin ‘yan majalisar 24 da jihar ke da su, suna kasa da shekaru 30, sai sauran da ke a tsakanin shekaru 30 zuwa 40.

Akwai dai kungiyoyi da dama a Nijeriya da ke fafutikar ganin an ba matasa damar shiga a dama da su a fannoni daban-daban.

Sai dai ko a watan jiya, an yi zargin aikin-kuruciya daga dan majalisar dattawan Nijeriya Sen. Abbo Elisha daga jihar Adamawa inda ake zargin ya ci mutuncin wata mata, da wasu ke alakanta hakan da karancin shekaru. Sai dai a jihar Zamfara shugaban majalisar jihar na fatan samuwar matasa ta haifar da daya-mai-ido a ayyukan su na majalisa.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply