Home Kasashen Ketare Jirgin kasa ya yi arangama da wata babbar mota a kasar Japan

Jirgin kasa ya yi arangama da wata babbar mota a kasar Japan

65
0

Abdullahi Garba Jani

 

Wani jirgin kasan fasinjoji mai gudun kilomita 120 a mintuna 60 ya yi karo da wata babbar mota a kudancin birnin Tokyo na kasar Japan.

Rahotanni sun ce bayan taho-mu-gamar da suka yi ne sai wuta ta tashi har ta yi sanadiyyar mutuwar mutum daya, mutane kusan 30 suka jikkata.

Jirgin kasar dai ya kai karo ga babbar motar ne ya kuma tura ta har zuwa ga wani bango, shi kuma jirgin ya samu matsala a wasu sassan jirgin da ya ke dauke da fasinjoji 500.

Kamfanin jirgin kasar ya ce ya kaddamar da bincike kan musabbabin faruwar hatsarin da ya wakana da safiyar Alhamis din nan.

Punch: Jani/dkura

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply