Home Kasashen Ketare Jirgin ruwa mallakin kasar Kamaru ya kife da fasinjoji kusan dari

Jirgin ruwa mallakin kasar Kamaru ya kife da fasinjoji kusan dari

73
0

 Hannatu Mani Abu/Jani

 

Jirgin ruwa mallakar kasar Kamaru ya kife da fasinjoji kusan dari da ma’aikatan jirgin dake ciki.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ruwan ya bar tashar terminal “C” da ke karkashin hukumar tashar jiragen ruwa ta Nijeriya wanda ke karkashin kulawar kamfanin Shoreline da ke birnin Calabar a jihar Cross River da ke kudancin Nijeriya a ranar Lahadin karshen mako.

Jirgin ya dauki hanyarsa ta zuwa kasar Kamaru sai dai kuma hatsarin ya faru da shi a gabashin tekun Atlantika.

Mai magana da yawun rundunar sojojin Nijeriya masu kula da ayukan jiragen ruwa Lieutenant A.A Amai, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch, sai dai yace ya zuwa yanzu ba su kai ga tabbatar da iya adadin mutanen da abin ya shafa ba.

An dai zargi cewa jirgin ruwan dankare ya ke da kaya wadanda wasu ke ganin cewa wannan dalilin na daga cikin abin da ya haddasa wannan hatsarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply