Home Sabon Labari Jirgin ruwa ya kife a jihar Neja, an samu mutuwa

Jirgin ruwa ya kife a jihar Neja, an samu mutuwa

91
0

Abdullahi Garba Jani/dkura

 

Hukumar kai daukin gaggawa ta jihar Neja ta tabbatar da mutuwar mutane uku da kwale-kwale  ya kife da su a Kogin Kaduna.

 

Shugaban hukumar Ahmad Inga ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a babban birnin jihar Minna.

 

Ya ce wani magidanci mai suna Yahaya Hamza da ‘ya’yansa biyu ne kwale-kwalen ya kife da su a lokacin da suke dawowa daga gona.

Hotan wani wanda jami’ai ke duba shi bayan ya samu hadarin jrigin ruwa a jihar Legas

Ahmad Inga ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 30 ga Agusta, 2019 a Kogin Kaduna a yankin Wuya kan hanyar Bida zuwa Mokwa, ya kara da cewa mutanen ‘yan asalin Karamar Hukumar Edati ne ta jihar Neja.

Sai dai shugaban hukumar ya ce mutumin da ke tuka kwale-kwalen ya tsira da rayuwarsa.  Ya yi nuni da cewa an gano gawarwakin wadanda suka mutu har ma an yi musu sutura.

 

Ahmad Inga ya shawarci masu amfani da jirgin kwale-kwale da su  rika daukar matakan kariya don kuwa gwamnatin jihar na kokarin samar da rigunan hana nutsewa cikin ruwa ga masu hawan kwale-kwale.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply