Home Kasashen Ketare Jonathan ya sake komawa Mali sasanci

Jonathan ya sake komawa Mali sasanci

108
0

Da yammacin Asabar din nan ne tawagar kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS karkashi jagorancin tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ta isa Bamako babban birnin kasar Mali domin ci gaba da yin sasanci a rikicin siyasar kasar, bayan da sojojin kasar suka hanbarar da gwamnatin shugaba Boubakar Keita a ranar Talatar makon jiya.

Tawagar dai ta isa birnin na Bamako bisa kokarinta na dawo da kasar Mali kan turbar dimokaradiyya.

Goodluck Jonathan tare da tawagarsa za su gana da Kanar Assimi Goita, wanda ya ayyana kansa a matsayin jagoran kungiyar da ta jagorancin juyin mulkin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply