Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS), ta nada tsohon shugaban Nijeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, a matsayin manzo na musamman da zai jagoranci wata tawagar yin sulhu kan dambarwar siyasa da ta ke faruwa a kasashen yammacin na Afirka da za a gudanar a cikin makon nan a kasar Mali.
Jonathan ya bayyana cewa zai yi bakin kokari don ganin cewa tawagar ta cimma matsaya da kuma samun nasara a taron da zai jagoranta.
