DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeKetare'Sojin Nijar sun dakile yunkurin juyin mulki a Yamai'

‘Sojin Nijar sun dakile yunkurin juyin mulki a Yamai’

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta ce ta dakile wani yunkurin bore da wasu sojoji suka yi a safiyar Asabar, bayan da aka ji harbe-harbe da karar bama-bamai a sassa daban-daban na babban birnin ƙasar, Yamai.

Ministan Tsaron Nijar, Janar Salifou Mody, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce wasu sojoji daga sansanin Base 101 ne suka bude wuta a wasu muhimman wurare a Yamai.

DCL Hausa ta ruwaito cewa rikicin ya fi kamari ne a kusa da fadar shugaban kasa da kuma sansanin sojin sama na Base 101, wanda ke kusa da Filin Jirgin Saman Kasa da Kasa na Diori Hamani.

Janar Mody ya ce dakarun tsaron kasar sun gaggauta daukar mataki tare da dakile boren, sannan suka sake karbe ikon wuraren da lamarin ya shafa. Ya kuma bukaci jama’a su kwantar da hankulansu su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

Shaidu da majiyoyin tsaro sun ce maharan sun yi yunkurin kutsawa cikin layin tsaron fadar shugaban kasa. Wasu bidiyoyi da aka wallafa a intanet kuma sun nuna motocin yaki masu sulke a wuraren da ke kusa da filin jirgin.

Bana Wagana Ibrahim, dan majalisar kawancen kasashen Sahel (AES), ya ce dakarun gwamnati sun yi nasarar fatattakar maharan daga Base 101. Wata majiyar tsaro ta ce an kashe wasu daga cikin maharan, yayin da wasu suka tsere kuma ake ci gaba da farautarsu.

Wannan shi ne karo na uku a bana da aka samu babban tashin hankali a yankin da ke kusa da filin jirgin sama da sansanin sojin Yamai, lamarin da ke kara nuna kalubalen tsaron da gwamnatin sojin Nijar ke fuskanta tun bayan juyin mulkin da ya kai ta kan mulki a shekarar 2023.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata