Home Sabon Labari Kaduna 2019: PDP ta bukaci da a ayyana dan takararta a matsayin...

Kaduna 2019: PDP ta bukaci da a ayyana dan takararta a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna

68
0

Daga Abdullahi Garba Jani

 

Jam’iyyar PDP da dan takararta a jihar Kaduna Isah Ashiru za su nemi kotun sauraran kararrakin zabe a jihar da ta soke kuri’u 515,951 da ake zargin cewa an kara  a yayin zaben gwamna na  9 ga watan Maris din da ya gabata

 

A gobe Litinin 19 ga watan Agusta, 2019 ne dai kotun sauraren kararrakin zabe a jihar Kaduna ta saka don bahasin karshe ga masu shigar da kara a zaben gwamnan jihar.

Isah Ashiru Kudan na jam’iyyar adawa ta PDP

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya samu kwafin takardun bayanan karshe na shigar da karar da PDP ta yi. A cikin takardun, PDP na bukatar da kotun ta ayyana Isah Ashiru a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da mafi ya rinjayen kuri’u na halal.

 

Masu shigar da karar dai sun gabatar da shaidu 135 daga cikin 685 da suka alkawarin gabatarwa don tuhumar nasarar da gwamna mai ci Mal Nasir El Rufa’i ya yi.

 

A bahasin nasu na karshe, masu shigar da kara, -PDP- sun zargi hukumar zabe ta Nijeriya -INEC- da kara kuri’u 391,741 ga dan takarar APC Nasiru El Rufa’i.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply