Home Labarai Kaduna: An ware ranaku 3 don zaman makokin rashin Sarkin Zazzau

Kaduna: An ware ranaku 3 don zaman makokin rashin Sarkin Zazzau

118
0

Gwamantin jihar Kaduna ta sanar da ware ranaku 3 domin zaman makokin rashin Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris da ya rasu a ranar Asabar.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El Rufa’i ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook.

Ya ce, za a bude wuraren aikin gwamnati, a Litinin da Talata, sai Laraba a zauna gida din yi wa marigayin adu’ar Allah Ya rahamshe shi.

Allah Ya karbi ran mai martaba sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris bayan da ya kwashe shekaru 45 yana sarautar Zazzau, inda ya rasu yana da shekaru 84.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply