Home Labarai Kaduna na bukatar bilyan 29 don magance tamowa

Kaduna na bukatar bilyan 29 don magance tamowa

120
0

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana bukatar kudi Naira bilyan 29 don magance matsalar cutar tamowa a jihar.

Shugaban kwamitin kula da ingancin abinci na jihar Mahmud Yamusa ya sanar da hakan a Kaduna.

Ya yi nuni da cewa akwai wagegen gibi a sashen inganta abinci mai gina jiki don shawo kan matsalolin tamowa da yara ‘yan kasa da shekaru 5 ke fama da ita a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply