Home Labarai Kakakin majalisar tarayya ya tallafawa ‘yan gudun hijirar Zamfara

Kakakin majalisar tarayya ya tallafawa ‘yan gudun hijirar Zamfara

137
0

‘Yangudun hijra: KAKAKIN MAJALISAR WAKILAI TA KASA YA TAIMAKA WA ‘YANGUDUN HIJRA DA MARAYUN JIHAR ZAMFARA.

Kakakin majalisar wakilai ta kasa Mr. Femi Gbajabiamilla ya ba da agajin kayan abinci ga marayu da ‘yangudun hijrar jihar Zamfara.

Kayan abincin sun hada da manyan motoci biyu shakare da shinkafa don rabawa ga ‘yangudun hijra da marayun jihar Zamfara.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, -NAN- ya ba da rahoton cewa, Mr. Femi Gbajabiamilla ya ziyarci jihar Zamfara ne don jajanta musu da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan kalubalen tsaron jihar.

Masharhanta daban-daban na ganin an dade ana ruwa kasa na shanyewa, ta yadda mutane ke ba da tallafi ga mabukata, amma ana zargin wasu tsirarun mutane su yi “uwa makarbiya” kan tallafin.

Wadanne hanyoyi za a bi don tabbatar da cewa wannan tallafi ya isa ga wadanda aka yi domin su?

#AgJ

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply