Home Lafiya Kamar dai jihar Kano, ana samun mace-mace da dama a Jigawa

Kamar dai jihar Kano, ana samun mace-mace da dama a Jigawa

92
0

Mutane da dama ne, yawancin su tsaffi, aka bada rahoton sun mutu a ƙaramar hukumar Haɗejia ta jihar Jigawa a cikin kwana huɗu.

Iyalan mamatan ne suka tabbatar da hakan ga Jaridar Daily Trust inda suka ce sun mutu ne tsakanin 1 zuwa 5 ga watan Mayu.

Mamatan dai sun mutu ne sakamakon zazzaɓi mai zafi, ciwon suga da hawan jini.

Saidai jami’an kiwon lafiya sun buƙaci hukumomi su zurfafa bincike kan alaƙar waɗannan mace-macen da kuma abun da ke faruwa ga maƙwabciyar jihar Kano.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply