Home Kasashen Ketare Kamaru: Kasuwar Bamenda Ta Yi Kwanaki 20 Da ‘Yan Aware Suka Kulleta...

Kamaru: Kasuwar Bamenda Ta Yi Kwanaki 20 Da ‘Yan Aware Suka Kulleta Duk Da Cewa Akwai Gwamnati

95
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”byfwo7k2k” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”ljpfii2s7f” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”utwplpisr7″ animation_delay=”0″]

A wannan Lahadi kasuwar Bamenda da ke Kudancin kasar Kamaru ta yi kwanaki 20 da kullewa. A cikin wannan lokaci babu wata hada-hada da ta gudana ta sayar da hatsi da sauran kayan masarufi.

Jaridar DCL Hausa ta tattauna da wani dan kasuwa wanda saboda dalilai na tsaro ba zamu bayyana sunansa ba. Dan kasuwar ya ce “indai ‘yan aware suka ce ba za’a yi kasuwa ba to ba za a bude ba. Mu a yanzu anan wallahi indai mutum daya cikinsu ya ce ba za a bude ba kamar wasa to kuma haka zai tabbata. Har yanzu kuma babu wani mataki da gwamnati ta dauka akan maganar. Ta na kallon su kawai su ma suna kallon gwamnati” acewar dan kasuwar a hirarsu da wannan jarida.

Kasuwar Bamenda dai ta kasance uwa-mabada-mama a fannin samar da kayan masarufi a cikin garin da ke kewaye. kasuwa ce da jama’ar yankunan karkara kan shigo don sayar da kayansu. Sai dai tunda rikicin ‘yan aware ya tilasta kulle kasuwar a baya-bayan nan, su kansu ‘yan kasuwar sun gaza samun sukunin zuwa kasuwannin kauye domin sarin-hatsi saboda acewar dan kasuwar da muka tattauna da shi, “dakarun ‘yan aware ba sa barin wani ya yi safara“. Rahotanni sun ce duk dan kasuwar da ya fusata ‘yan awaren to akwai yiwuwar za su iya yi masa yankan rago. Yan kasuwa dai na zullumin budewa saboda tsoron ‘yan ware za su kona musu kaya idan suka bijirewa umarninsu.

Sai dai kuma sabanin abin da wannan dan kasuwa ya shaida mana, wani dan jarida a Bamenda Baba Abdullahi ya ce duk kullewar da aka yiwa kasuwar, akan bude ta a ranakun Asabar ayi hada-hadar da ba a rasa ba.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya wanda ke yaki da kungiyar Ambazoniya mai fafutukar kafa wata kasa ta daban daga kasar Kamaru

Tun a shekara ta 2016 wasu jama’a da suka kira kansu masu son kafa kasar Ambazoniya mai magana da harshen Turanci suka fara rikici da gwamnatin Kamaru a yunkurinsu na mayar da Kudancin Kasar  a matsayin kasa mai cin gashin kanta. Tun daga lokacin rikicin ya yi ta ruruwa har ta kai ga ya taba muhimman abubuwan rayuwa na jama’ar yankin kamar karatu da sauransu. Sai kuma ga shi yanzu abin ya zo ya ga hada-hadar kayan masarufi.

Yunkurin kawo sulhu a rikicin na Kamaru na ci gaba da fuskantar cikas. Manyan mutane irinsu fitaccen dan siyasa John Fru Ndi sun yi kokarin sasantawa amma kuma ‘yan awaren suka zarge shi da zama dan amshin shatar gwamnati.

 

 

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply