Home Coronavirus Kamfanin BUA ya tallafa wa Nijeriya da rigakafin corona milyan 1

Kamfanin BUA ya tallafa wa Nijeriya da rigakafin corona milyan 1

37
0

Kamfanin BUA, ɗaya daga cikin manyan kamfanoni a Afirka, ya ce ya biya kuɗin allurar rigakafin cutar corona guda miliyan 1 na kamfanin AstraZeneca da za a kawo Nijeriya ta hanyar shirin rigakafin AFREXIM tare da haɗin gwiwar CACOVID.

A cewar wata sanarwa da mai kula da harkokin hulda da jama’a a Kamfanin, Otega Ogra ya sanya wa hannu, yace za a rarraba alluran rigakafin kyauta ga ‘yan Nijeriya ba tare da karbar sisin kwabo ba.

Shugaban kamfanin Abdulsamad Rabi’u ya gode wa Shugaban Bankin Afrexim, Dokta Benedict Oramah da ya ba da damar sayan rigakafin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply