Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Kamfanin masaka na Kaduna ya kori ma’aikata 300 

Kamfanin masaka na Kaduna ya kori ma’aikata 300 

117
0

Kamfanin masaka dake jihar Kaduna ya tasamma durkushewa sakamakon korar ma’aikata 300 da ya yi, wanda ya lamushe kashi 30% na karfin ma’aikatan kamfanin.

Tuni dai daruruwan kamfanoni suka rufe masana’antunsu dake a jihar ta Kaduna sakamakon rashin ingantaccen yanayin aiki da kuma tsadar kayan aiki.

Majiyar DCL Hausa ta binciko cewa tsohuwar Masakar an kafa ta tun shekarar 1964 tana kuma da rassa da yawa a wannan yankin.

Masana’antar an taba rufe ta a shekarar 2007 ta dawo aiki a shekarar 2010 amma tun daga wannan karon take funskantar matsaloli daban-daban.

Shugaban kungiyar masana’antu na kasa John Adaji ya shaida cewa kakkabar ma’aikatan ta biyo bayan tattaunawa da suka yi da masana’antar, kuma za su tabbatar ma’aikatan da aka kora sun karbi dukkan hakkokinsu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply