Kamfanin Pfizer and BionTech zai kai zangon farko na kason rigakafin cutar Covid-19 a Canada, cikin watan nan.
Firaministan kasar Justin Trudeau ya shaida wa wani taron manema labarai a ranar Litinin cewa Canada ta cimma yarjejeniya da kafanin na Pfizwer don fara shigo da maganin da wuri.
Ya ce Canada za ta samu rigakafin har 249,000 a cikin watan Disamba kafin daga bisani a kawo sauran a cikin shekarar 2021.
