Gamayyar ɓangarori masu zaman kan su ƙarƙashin kulawar babban bankin Nijeriya, sun tara ₦25,893,699,791 domin yaƙi da Covid-19.
Bayanan da babban bankin ya fitar ya nuna cewa, zuwa ranar 17 ga watan Afrilu ne aka tara kuɗaɗen daga kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane 107.
Idan dai za a iya tunawa a ranar 26 ga watan Maris ne, gwamnan CBN Godwin Emefiele ya ƙaddamar da kwamitin a wani mataki na shirye-shiryen bankin na yaƙi da cutar.
