Home Labarai Kananan hukumomi 101 za su fuskanci ambaliyar ruwa a Nijeriya

Kananan hukumomi 101 za su fuskanci ambaliyar ruwa a Nijeriya

191
0

Hukumar ba da agajin gaggawa NEMA ta yi gargadin cewa akwai yiyuwar samun ambaliyar ruwan a kananan hukumomi 101 da ke fadin kasar nan.

Shugaban hukumar Air Vice Marshal Muhammadu Muhammed (Rtd.) ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fito da hukumar.

Ya kuma kara da cewa sun sami wannan bayani ne daga hukumar kula da yanayin zubar ruwan sama Nimet.

Sanarwar ta bayyana cewa yankin karamar hukumar Zaria a jihar Kaduna na daga cikin yankunan da za su fuskanci ambaliyar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply