Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kafa wani kwamiti na mutane biyar da zai binciki daya daga cikin jami’anta, da ake zarginsa da yin mu’amala tare da matar aure a dakin otal.
Babban kwamandan Hisbah na jihar, Ustaz Haruna Ibn-Sina, ya tabbatar da cewa an ba kwamitin wa’adin kwanaki 3 da ya binciki lamarin.
“Na kafa kwamitin bincike kuma na ba shi wa’adin kwanaki 3 ya gabatar da rahotonsa. Na kuma gayyaci duk bangarorin da abin ya shafa su dauki bayanansu” inji Ibn-Sina.
Jami’an ‘yansanda na yankin Noman’s Land ne dai su ka kama Rimo a cikin wani karamin otal a yankin jan wuta a Sabon Gari.
Majiyoyin ‘yansanda sun ce sun dauki matakin ne bisa bayanan sirri da suka samu, sun kuma tabbatar da cewa sun same shi tare da matar a cikin dakin.
