Home Sabon Labari Kano: An kashe matarsa, an jefa ‘yarsa a rijiya

Kano: An kashe matarsa, an jefa ‘yarsa a rijiya

98
0

 

Daga Nasiru Salisu Zango

A wayewar garin yau wani magidanci ya dawo gidan sa ya iske kofar gidan a rufe. Bayan ya buga ba a bude ba, sai ya nemi makota suka taimaka. Daga nan sai aka balle kofar gidan, kuma ana shiga sai aka iske matarsa a kwance an yanka ta, ita kuma “yar aka neme ta aka rasa.

Daga bisa aka duba rijiyar gidan aka dauko gawar ta ita yarinyar.

Yanzu Haka ‘yar da uwar duka sun rasu. Allah yayi musu rahma.

SHARHI

Babban abin da yake bani tsoro shi ne karuwar irin wadannan matsaloli, da kuma yadda idan sun faru sai dai ayi jimami a wuce, ba tare da mun hada kai wajen magance matsalar ba.

Karuwar matasa masu gararamba a gari babbar matsala ce da ka iya haifar da irin wadannan matsaloli. Mu hada kai kada wannan bala’i ya gama da mu gaba daya. Allah ya maganta mana.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply