Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyarsu, APC ce za ta lashe dukkanin kujeru 44 na shugabannin kananan hukumomi da kansiloli 484 a zabukan kananan hukumomi da ke gudana a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya samu damar jefa kuri’arsa a mazabarsa ta 008 a garin Ganduje, karamar hukumar Dawakin Tofa da ke jihar.
A cewarsa, jam’iyya mai mulki ce za ta lashe dukkanin kujerun bisa la’akari da ‘yawan fitowar jama’a” da ya gani a cibiyar.
Ya kara da cewe APC za ta lashe zaben ne ta hanyar zunzurutun kuri’u, ba da karfi ko tursasawa ba” Inji shi.

To nidai nace bagiringirinba taimai zaban kananan hukumomi a jahar kano.