Home Sabon Labari Kano: Hukumar Hisbah Ta Kama Mabarata 262 Cikin Watan Agusta

Kano: Hukumar Hisbah Ta Kama Mabarata 262 Cikin Watan Agusta

70
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”oy4gc50na” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”9u8l6iolxu” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”fvy9svkt6j” animation_delay=”0″]

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta ce ta kama mabarata 262 a watan Agusta cikin kwaryar birnin Kano bisa zargin sun yi wa  dokar hana barace-barace ta jihar karan-tsaye.

 

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Malam Lawan Ibrahim ya fada wa manema labarai cewa daga cikin wadanda aka kama din akwai 175 manya da 87 kananan yara, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta labarta.

 

Malam Ibrahim ya ce an yi wannan kamen ne a ya yin samamen da hukumar ke kai wa a sassa daban-daban na birnin. Ya ci gaba yana cewa an kai samamen a unguwannin kan hanyar Ajasa, Lodge Road, Kantin Kwari, Railway, Sabon Gari da sauran hanyoyin cikin birnin.

 

Daga cikin yawan wadanda aka kama din, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na hukumar ya shaida, akwai mabarata 100 da aka tabbatar ‘yan asalin jihar Kano ne, sai 158 daga Bauchi, Katsina, Sokoto, Borno da Jigawa, sai guda 2 daga kasar Ghana, da wasu biyu daga Jamhuriyar Nijar.

 

Ya ce sun samu 3 daga cikin mabaratan da suka kama da tabin hankali, inda ya ci gaba yana cewa za a mayar da wadanda ba ‘yan asalin Kano ba garuruwansu na asali.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply