Home Lafiya Kano: Masu ciwon sikila 80 suka mutu saboda rashin kudin sanya musu...

Kano: Masu ciwon sikila 80 suka mutu saboda rashin kudin sanya musu jini

75
0

Kungiyar masu fama da ciwon sikila ta Kano Sickle Cell Club ta ce mambobinta guda 80 sun mutu a shekarar 2019 a sakamakon rashin kudin da za su sayi jinin da za a sanya musu.

Malam Abdulkadir Muhammad Sakataren kungiyar ya shaida wa manema labarai a Kano cewa mutuwar wadannan mutane ta faru a sakamakon rashin kudi. Ya ce rashin kudin magani yayi musu katutu, hatta kudin mota da masu fama da irin wannan larura za su je asibiti ana wayar gari babu.

Kungiyar masu fama da ciwon sikilan ta ce cutar sikila tana da dawainiya sosai domin ta kan cinye kusan duk dukiyar mutum ko kuma iyayen yaran da ke  wannan jinya. A don haka lamarin ya kai wanda  gwamnati da jama’an gari za su kawo musu agaji na gaggawa . Kungiyar ta ce akwai mutanensu da an rubuta musu magani amma kuma sun kasa saye, ciwon na nan na cinsu.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Sai dai daraktan da ke kula da harkokin lafiya a Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano, Dr Shehu Abdullahi ya ce gwamnati na iyakar kokarinta wurin ganin ta magance matsalolin da masu cutar sikila ke fuskanta.Ya ce gwamnati ta ware Naira  Milyan 50 don kula da masu wannan ciwo. Bayan haka kuma akwai cibiyoyi na musamman da aka ware don masu cutar sikila kawai. Ga kuma likitoci da aka tura kasashen waje don kara gogewa a kan yadda za a yaki wannan cuta.

To amma da alama duk wannan zai kasance kamar roman baka ne ganin cewa wadanda aka ce ana yi wa tanadin sun ce ba su gani ba, hasali ma su na korafin masu ciwon sikila na mutuwa a saboda da rashin kudin da za su sayi jini da sauran magunguna.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply