Home Labarai Kano: Matuka A daidaita sahu sun janye yajin aiki

Kano: Matuka A daidaita sahu sun janye yajin aiki

27
0

Matuka babura masu kafa uku da aka fi sani da A daidaita sahu a Kano sun sanar da janye yajin aikin dauka fars biyo bayan tsoma hannu da kungiyar kwadago ta yi da sauran kungiyoyi.

A ranar Litinin din makon nan dai kungiyar ta tsunduma yajin aiki don nuna kin amincewa da biyan harajin Naira 100 da gwamnatin Kano ta saka musu ta hannun hukumar KAROTA.

DCL Hausa ta rawaito cewa wannan yajin aiki da ‘yan a daidaita sahu suka shiga ya jefa dubban mutane cikin wahalhalu na zuwa kasuwa da wuraren aiki da dalibai ‘yan makaranta.

A taron manema labarai a ofishin KAROTA, shugaban kungiyar kwadago na Kano, Ado Minjibir ya shaida cewa bangarorin biyu sun cimma matsaya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply