Home Labarai Kano ta hana shige da fice daga Juma’ar nan

Kano ta hana shige da fice daga Juma’ar nan

74
0

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bada umarnin rufe duk hanyoyin shigowa jihar.

Wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai ya fita da yammacin jiya, ya ce gwamnan ya kuma bada umarnin rufe filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano.

Sanarwar ta ce wannan umarni zai fara aiki ne daga ranar Juma’a 27 ga watan Maris da ƙarfe 12:am na dare.

Sanarwar ta kuma shawarci duk wanda ke son shiga Kano daga wata jiha ko kuma yake son barin Kano to ya yi hakan tsakanin yau Alhamis da kuma gobe Juma’a.

Sanarwar ta kara da cewa Gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne domin kare al’ummar jihar Kano daga kamuwa da wannan cutar corona wato Covid-19 da ake fama da ita a duniya baki daya.

Kawo yanzu dai ba wanda ya kamu da cutar a jihar Kano.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply