Hukumar jin daɗin Alhazai ta Kano ta ce ta sayar da dukkan kujerun aikin Hajjin 2027 guda 3,050 da aka ware wa jihar.
Daraktan-Janar na hukumar, Abubakar Ibrahim Matawalle ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a Kano, inda ya ce an samu nasarar kammala sayar da kujerun ne bayan ci gaba da jan hankalin maniyyata da su biya kuɗaɗen Hajji tare da kammala takardun da ake buƙata.
Sai dai ya bayyana cewa sama da maniyyata 200 na cikin jerin masu jiran gurbi, bayan sun mallaki fasfo na ƙasa da ƙasa tare da kammala biyan kuɗaɗen da ake buƙata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Matawalle na gargadi waɗanda suka gaza kai fasfon kafin wa’adi ya cika cewa za su iya rasa gurbin da aka ware musu, duk da cewa sun riga sun biya kuɗin Hajjin.
Ya ce an sanya wa’adin ne domin hukumar ta samu damar kammala shigar da bayanan maniyyata da kuma sauran matakan tantance takardu da neman bizar Hajji bisa buƙatun NAHCON.
Daraktan-Janar ɗin ya kuma yi gargadin cewa idan ba a yi amfani da dukkan kujerun da aka ware wa Kano ba, za a iya janye wasu daga cikinsu a sake bai wa wasu jihohi.
A wani ɓangare kuma, hukumar na sake duba yadda za ta tsara masaukin alhazan Kano, inda ake shirin rage gidajen da ake amfani da su daga kusan gida tara ko 10 zuwa gida biyu kacal.
A cewarsa, wannan sabon tsarin zai sauƙaƙa wa hukumar kula da alhazai tare da samar musu kayayyakin jin daɗi kamar abinci, kula da lafiya da sauran hidimomi.
Matawalle ya ce hukumar na ƙoƙarin inganta ayyukan da za ta yi wa alhazan Kano a Hajjin 2027, tare da amfani da darussan da aka koya daga ƙalubalen da aka fuskanta a Hajjin da ya gabata.
Ya kuma tuna cewa a Hajjin da ya gabata, Kano ta samu nasarar kammala bizar alhazai 3,600 gaba ɗaya bayan jami’an hukumar sun yi aiki dare da rana domin cika wa’adin shigar da bayanan fasfo.
