Shugaban gidauniyar fansho ta jihar Kano Sani Gabasawa ya ce tsaffin ma’aikatan jihar na bin kuɗin sallama da suka haura Naira Biliyan 20.
Gabasawa ya bayyanawa ƴan jarida haka ne a ranar Alhamis lokacin da yake maida martani kan zargin suna sasantawa d tsaffin ma’aikatan wajen bashi wani kaso kafin a biya su kuɗin sallamar.
A cewar sa gidauniyar bata samu damar biyan kuɗin sallamar ma’aikata ba tun daga shekarar 2016, wanda hakan ya sa yawan kuɗin da ake bin jihar ya kai Biliyan ₦20 ga yawan ma’aikata 31,000.
Saidai kuma ya alaƙanta matsalar ga kasawar wasu hukumomin gwamnati na bada kashi 8 na kuɗin fanshon yayin da wasu hukumomin suka bada giɓi.
