Home Labarai Kano za ta kashe ₦3.2bn kan zaɓen ƙananan hukumomi

Kano za ta kashe ₦3.2bn kan zaɓen ƙananan hukumomi

125
0

Gwamnatin jihar Kano za ta kashe kimanin Naira biliyan 3 da miliyan 200 a zaben ƙananan hukumomin jihar 44 da za a yi ranar 16 ga Janairu, 2021.

Malam Muhammad Garba, shi ne kwamishinan yaɗa labarai na jihar, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Alhamis.

A farkon makon nan ne hukumar zaɓen jihar, KANSIEC, ta tsayar da ranar 16 ga Janairun baɗi a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomi guda 44 a jihar da ma kansilolinsu 484 bisa wa’adin shekaru uku ga wadanda suka yi nasarar lashe zaɓen.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply