Manyan ƙungiyoyin farar hula a jihar Kano sun yi fargabar cewa jihar Kano za ta zamo fagen mace-mace sakamakon cutar Covid-19 idan har gwamnatin tarayya ba ta ɗauki matakan da suka dace ba kan halin da jihar ke ciki.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata buɗadɗiyar wasiƙa da ƙungiyoyin 12 suka sanya wa hannu kuma aka aikewa sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban ƙasa na yaƙi da Covid-19.
Sama da mutum 600 ne dai suka rasa rayukansu a birnin Kano a cikin kwanaki 7, wanda har yanzu ba a tabbatar da dalilan mace macen ba.
