Home Addini #Kano9 : Ba A Samu Iyayen Yara 2 Cikin 9 Da Aka...

#Kano9 : Ba A Samu Iyayen Yara 2 Cikin 9 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Zuwa Anambra Daga Kano Ba

77
0

Kwamandan yaki da kidinafin a rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, CSP Babagana Saje ne ya tabbatar da haka ga gwamnatin jihar Kano a lokacin da yake hannanta yaran da aka yi garkuwa da su daga Kano zuwa jihar Anambra ga gwamnati.

 

CSP Saje ya ce yana sanar da duk iyayen da yaransu kanana suka bace ko kuma aka yi kidinafin dinsu da suyi kokari su zo su duba yaran don ganin ko ‘ya’yan nasu na cikin yaran Kano da aka gano anyi garkuwa da su zuwa Anambra aka canza musu suna, aka mayar da su Kiristoci.

 

Jami’in ‘yan sandan ya shaida wa gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje cewa 1 daga cikin yaran 9 yanzu haka yana asibiti yana jinya saboda ba shi da lafiya. A saboda haka a yanzu yara takwas ‘yan sanda za su iya gabatarwa gwamnatin jihar har zuwa lokacin da dayan ya samu lafiya.

Saje ya kuma ce da zarar ‘yan sanda sun kammala bincike za su hanzarta kai wadanda ake zargi da akai ta wannan mummunan aiki na garkuwa da kananan yara da sauya musu addini kotu.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya-NAN- da ya bayar da wannan labari ya ce Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Alhaji Usman Alhaji, wanda ya wakilci gwamnan jihar, ya shawarci iyayen da suka ga ‘ya’yansu da kada su rinka bari ‘yan jaridu da kungiyoyin sa-kai na NGOs na yawan tattaunawa da su don gudun kada wasu su yi amfani da damar wurin sake cutar da yaran nasu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply