Home Coronavirus Gwamnati: Ka da ‘yan Nijeriya su sakankance don an sassauta dokar Covid-19

Gwamnati: Ka da ‘yan Nijeriya su sakankance don an sassauta dokar Covid-19

94
0

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban ƙasa na yaƙi da cutar Covid-19, Boss Mustapha, ya gargaɗi ƴan Nijeriya kan nuna halin ko in kula a lokacin sassauta dokar hana fita da da gwamnati ke shirin aiwatarwa.

Da yake magana a Abuja, lokacin bada jawaban kwamitin, Mustapha ya ce a daidai lokacin da za a fara sassauta dokar a ranar Litinin, ya kamata ƴan Nijeriya su samu bayanan yadda za su kare kansu, kuma su yi amfani da bayanan.

Ya kuma bayyana buƙatar da ke akwai na jihohi, hukumomin tsaro, ƙungiyoyin ƴan kasuwa, kamfanoni da sauran ƴan ƙasa, kowa ya fahimci irin alhakin da ke kansa na murkushe cutar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply