Home Labarai Karairayin gwamnati ba za su sa mu janye yajin aiki ba –...

Karairayin gwamnati ba za su sa mu janye yajin aiki ba – ASUU

164
0

Kungiyar malaman jami’o’i ta Nineriya ASUU ta ce dukkanin karairayi da farfagandar da gwamnati ke yadawa ba za su sa ASUU ta janye yajin aikin da ta ke ciki ba.

Kungiyar ta musanta batun da ministan kwadago da ingantuwar aiki Chris Ngige ya yi cewa kungiyar ta janye yajin aikin da ta shafe watanni 6 tana yi.

Shugaban kungiyar reshen jami’ar Ibadan Prof Ayoola Akinwole ya ce irin wadannan maganganun za su ma kara dagula lamurra, ba wai kawo maslaha ba.

Prof Ayoola a cikin wata takarda ya jaddada cewa kungiyar ba ta janye yajin aikin da ta ke yi ba, har dai gwamnati ta biya musu bukatun su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply