Home Labarai Karanta cikakken bayani game da daftarin kasafin kudin 2020 na jihar Katsina

Karanta cikakken bayani game da daftarin kasafin kudin 2020 na jihar Katsina

105
0

Gwamnan jihar Katsina Alh Aminu Bello Masari ya gabatar da daftarin kasafin kudin 2020 na Naira bilyan 249,463,829,250 a gaban majalisar dokokin jihar.

Kasafin kudin 2020 dai ya fi na shekarar 2019 da Naira bilyan 48,721,868,505.

Daftarin kasafin kudin kamar yadda gwaman Aminu Masari ya bayyana na da taken tuna baya da kuma inda aka dosa.

Alh Aminu Bello Masari ya yi bayanin cewa an tsara kasafin kudin 2020 da cewa ayyukan yau da kullum na da Naira bilyan 75, 579,865,990, manyan ayyuka na da Naira bilyan 173,883,963,260.

Kazalika, gwaman ya ce ana kyautata zaton samun Naira bilyan185,346,417,590 don aiwatar da kadssadin kudin, da ya hada da samun Naira bilyan 12,246,560,000 daga kudadwn shiga na cikin gida, da Naira bilyan 34,099857,590 daga sauran hanyoyin kudaden shiga da kuma naira bilyan 139,000,000,000 daga daunin gwamnatin tarayya.

Ya yi nuni da cewa an samu karin kudaden shiga a kasafin kudin 2020 da kaso 17.9% sama da na 2019. Bugu da kari, yawan kudaden ayyukan yau da kullum sun Karu da kaso 23.7% , da hakan ya nuna cewa an samu karin kudaden shiga da kaso 17.9 ga kasafin kudin 2019.

Gwamnan ya kara da cewa ayyukan ci gaban gwamnatinsa sun hada da inganta ilmi, samar da Ruwan sha, inganta aikin Gona, inganta lafiya, da sauransu.

A hakan ne gwamnan ya ce an ware Naira bilyan 24,368,255 ga sashen ilmi, da naira bilyan 23,020,086,250 ga sashen lafiya, da kuma naira bilyan 13,624,000,000 ga aikin samar da Ruwan sha.

Bugu da kari, akwai Naira bilyan 13,1115,509,500 ga aikin Gona, aka kuma ware naira bilyan 23,414,464,410 ga aikin Gina hanyoyi, da kuma naira bilyan 30,149,885,405 ga sashen inganta muhalli.

Daga karshe gwamnan ya yi Godiya ga sarakuna da malaman addini a fading jihar bisa kokarin da suke yi ma tabbatar da jihar Katsina ta samu ci gaba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply