Home Kasashen Ketare Karanta yadda Shugaban kasar Mali ya sanar da murabus dinsa

Karanta yadda Shugaban kasar Mali ya sanar da murabus dinsa

179
0

A daren Talatar nan, shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya bayyana murabus din sa ta kafar talabijin din kasar kai tsaye daga sansanin sojoji da ake tsare da shi.

Wannan murabus dai ya biyo bayan shafe tsawon sa’o’i da shugaban kasar ya yi a hannu sojojin kasar tare da mambobin gwamnatin shi bayan wani bore daga ‘yan kasar da ma sojojin a yinin jiya Talata.

Dama kafin murabus din, wasu kungiyoyi da wasu manyan kasashe suka yi tir da matakin sojoji na cabke shugaban kasar da sauran mambobin gwamnatinsa.

Sojojin sun ce za su mika ragamar mulkin ga farar hula nan ba da jimawa ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply