Home Sabon Labari Karfin Aikin Jarida ya sa Femi Kayode janye kalamansa

Karfin Aikin Jarida ya sa Femi Kayode janye kalamansa

117
0

Fitaccen dan siyasar Femi Fani Kayode ya wallafa bidiyo a safiyar Larabar nan yana cewa jaridar DailyTrust da wakilinta na jihar Cross Rivers sun masa karya biyo bayan bidiyon da ake yada wa da ya nuna yadda dan siyasar na PDP ke cin mutumcin dan jaridar saboda tambayar dan jaridar ta cewa “shin Femi Kayode wane ne ke daukar dawainiyar ayyukanka?“

Nan take Femi ya fara zage-zage yana mai kiran dan jaridar da sunayen da ba su dace ba. Sai dai bada jimawa ya janye kalamansa.

To amma  wannan ba sabon abu bane domin a makonnin baya DCL Hausa ta kalli wani bidiyo inda Femi Kayode ke yin tir da irin wannan tambaya da wani dan jarida a jihar Zamafara ya yi masa.

Sai dai a safiyar Larabar nan tsohon ministan sufurin sama a Nijeriya ya ce yana mai janye kalmar „“stupid“ da ya yi amfani da ita a kan dan jaridar. Janye kalaman nasa ya biyo bayan yadda jaridun Nijeriya daga ranar Talata zuwa Larabar suka yi „ca“ a kan dan siyasar da ya kware wurin sukar gwamantin Shugaba Buhari.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply