Home Labarai Karin Albashi: NLC Ta Ce Ba Gudu Ba Ja Da Baya Akan...

Karin Albashi: NLC Ta Ce Ba Gudu Ba Ja Da Baya Akan Tafiya Yajin Aiki Ranar 16.10.2019

73
1

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”akwuxo2bo7″ data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”64j4weyio” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”g9tiig8ufe” animation_delay=”0″]

Kungiyar Kwadigo ta Nijeriya, NLC ta ce babu gudu ba ja da baya a yunkurinta na tafiya yajin aikin da ta tsara tsunduma a ranar Laraba 16.10.2019.

 

A cikin wata wasikar tunasarwa da kungiyar ta NLC mai dauke da sa hannun sakatare janar na kungiyar Mr Emmanuel Ugboaja, ya fitar, NLC  ta umarci shugabannin kungiyar kwadago na jihohi da su tafi yajin aiki kamar yadda aka tsara madamar ba su cimma matsaya da gwamnati ba a taron da za su yi a ranar Talata 15 ga watan Oktoba.

 

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, NAN, ya ce takaddama tsakanin gwamnatin tarayyar Nijeriya da kungiyar kwadigo ta yi kamari ne a kan aiwatar da sabon tsarin albashi na Naira 30,000 mafi karanci ga kowane ma’aikaci.

 

‘Yan kungiyar kwadago sun bukaci gwamnati ta yi karin albashi na kaso 29 cikin 100 na albashi ga ma’aikatan da ke matakin albashi na 07 zuwa na 14. Ta kuma nemi a kara wa ma’aikatan da ke matakin albashi na 15 zuwa 17 karin kaso 24 na albashinsu.

 

To sai dai gwamnati ta ce wannan bukata ba mai yiwuwa ba ce, inda ta ce karin kaso 11 cikin 100 na albashi za ta iya yi wa ma’aikatan da ke matakin albashi na 07 zuwa 14, yayin da za ta kara wa ma’aikatan da ke matakin albashi na 15 zuwa 17 kaso 6.5.

 

Fiye da watanni shida da suka gabata ne dai gwamnatin tarayya ta amince da karin albashi na Naira 30,000 a matsayin mafi karanci amma kuma aiwatarwa ta zama jidali.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply