Home Labarai Karin aure na kawo karin talauci-Sarkin Anka

Karin aure na kawo karin talauci-Sarkin Anka

88
0

[cmsmasters_row][cmsmasters_column data_width=”1/1″][cmsmasters_text]

Mai martaba Sarkin Anka a jihar Zamfara Alhaji Attahiru Ahmad, ya ja kunnen masu karamin karfi da su guji kara aure alhalin ba su iya daukar nauyin iyalansu na gida ba.

Alhaji Ahmad da ya yi wannan jan kunnen a garin Anka, ya ce yawan aurace-aurace na gurgunta tattalin arziki, kuma yana kara wa marasa karfin da suke kara auren bakin talauci.

Sarkin dai na magana ne a lokacin rabon kayan tallafin gudanar da sana’o’in hannu ga wadansu mata da uwargidan gwamnan jihar Zamfara ta samar.

Basaraken ya ce har kananan ma’aikatan gwamnati na irin dabi’ar yawan aurace-auracen da kan iya kai su ga halin gaza kula da iyalin.

Ya ci gaba yana cewa hakan ne ke haddasa karuwar yawan yara da ba sa zuwa makaranta, saboda iyayensu ba su iya daukar nauyinsu.

Alhaji Ahmad ya roki mutane da su rika yin aure kwatankwacin yawan samun da suke yi don tabbatar da ‘ya’yansu sun samu nagartaccen ilmi da tarbiyya mai kyau.

Jaridar The Punch ta ce a wurin taron an rarraba kayan ne ga matan da suka fito daga kananan hukumomin Anka, Bakura, Bukkuyyum, Gummi, Maradun da Talata-Mafara na jihar.

Daga karshe ya bukaci matan da suka amfana da su yi amfani da kayan don su dogara da kansu.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply