Home Labarai Karin farashin lantarki ba zai shafi talaka sosai ba

Karin farashin lantarki ba zai shafi talaka sosai ba

124
0

Hukumar da ke kula da kayyade farashin hasken wutar lantarki ta Nijeriya (NERC) ta jaddada cewa karin farashin da ta ke shirin yi ba zai shafi talakawa masu karamin karfi sosai ba.

Shugaban hukumar Farfesa James Adeche Momoh ya sanar da haka lokacin da ya kai wata ziyarar aiki a majalisar dattawa ta kasa.

Ya kuma tabbatar wa majalisar cewa hukumar ta kara farashin lantarki ne ta yadda ba za a kuntata wa al’ummar ba, ya kuma ce tuni hukumar ta bullo da wani sabon tsari da zai tabbatar da cewa karin bai shafi masu kananan sana’o’i sosai ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply