Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya aike da karin sunayen mata 2 a zauren majalisar dokokin jihar don tabbatar da su a matsayin kwamishinoni a jihar.
Maryam Garba Bagel daga karamar hukumar Dass da Dr Asma’u Ahmed Giade daga karamar hukumar Giade, ne aka aike da sunayensu a majalisar dokokin jihar.
Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Bauchi Malam Ladan Salihu ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook.
