Home Labarai Karon farko cutar coronavirus ta bulla Afrika

Karon farko cutar coronavirus ta bulla Afrika

59
0

An samu bullar cutar coronavirus a wani mutum dan kasar waje a kasar Masar, wanda aka kebance shi, shi kadai a asibiti kamar yadda Reuters suka ruwaito.

A wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta fitar ta c eta gaggauta sanar da hukumar lafiya ta duniya WHO kuma an dauke dukkan matakan da suka dace na hana yaduwar cutar.

Da take tabbatar da lamarin, WHO a yankin gabas, ta ce mutumin da ya kamu da cutar bai nuna wasu alamun kamuwa da cutar ba, kumma yana cikin yanayi mai kyau.

Hukumar lafiyar ta bada wannan tabbacin ne bayan hukumomin Masar sun tabbatar da bullar cutar a karon farko cikin kasar, tana mai cewa suna aiki tare da hukumomin lafiya na kasar kan bincike da kuma daukar mataki kan barkewar cutuka.

Da wannan rahoto dai, yawan wadanda suka kamu da cutar a yankin kasashen larabawa ya kai 9 inda kasar UAE take da 8 Masar ke da guda.

Duk da cewa akwai fargabar bullar kwayar cutar a nahiyar Afrika, wannan rahoto da aka samu a Masar shi ne na farko da aka tabbatar cutar ta bulla a nahiyar.

A rahoton da take fitarwa ko wace rana WHO ta ce yanzu haka mutum 47,505 aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar China da suka hada da mutum 16,427 a lardin Hubei.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply