Home Labarai KAROTA ta kama mota dauke da tabar wiwi ta kimanin milyan 30

KAROTA ta kama mota dauke da tabar wiwi ta kimanin milyan 30

51
0

Hukumar KAROTA a jihar Kano ta ce
ta yi nasarar cafke wata mota kirar Golf’ dauke da tabar wiwi da aka kiyasta kudinta zai kai kimanin Naira miliyan 30.

Shugaban hukumar Baffa Babba Dan Agundi ya bayyana cewa jami’ansu, sun kama motar a kofar Kansakali zuwa kofar Dawanau da misalin karfe 3:30 na daren Talata wayewar Laraba.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa tuni mutanen da ke cikin motar suka tsere.

Dan Agundi ya ce ya ba da umurnin mika motar a hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi reshen jihar Kano ta NDLEA domin daukar matakin da ya dace.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply