Gwamnatin tarayya ta hana wasu ‘yan Nijeriya 100 fita kasashen waje saboda karya dokokin kariya daga COVID-19.
Kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar ya sanar da hakan ranar Talata, a shafinsa na Twitter.
Kwamitin ya kuma saki bayanan fasgo na mutanen da aka haramtawa tafiye-tafiyen, yana mai cewa takunkumin hana fita kasar da aka sa masu na tsawon watanni shida ne daga 5 ga watan Fubrairu, zuwa 30 ga watan Yulin 2021.
