Home Coronavirus Karya dokar Covid-19: Kamfanonin jiragen za su biya tarar $3,500/fasinja a Nijeriya

Karya dokar Covid-19: Kamfanonin jiragen za su biya tarar $3,500/fasinja a Nijeriya

95
0

Ma’aikatar kula da sufurin saman Nijeriya ta yi barazanar cin tarar kamfanonin jiragen sama $3,500 kan duk fasinjan da ya karya dokokin kare yaɗuwar cutar Covid-19 da kwamitin shugaban ƙasa na yaƙi da cutar ya kafa.

A cikin wata takarda da aka aike wa kamfanonin ɗauke da sa hannun Babban Daraktan Ma’aikatar Capt Musa Nuhu ta umurci fasinjoji daga UK da kuma Afirka ta Kudu su gabatar da takardar izinin tafiya, da kuma sakamakon gwajin Covid-19 da aka yi masu cikin sa’o’i 96 kafin su taso.

Takardar ta ce an ɗauki matakin ne domin daƙile yaɗuwar cutar da ke bazuwa a faɗin duniya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply