Home Labarai Kasafin ƴan sanda na 2021 ya yi kaɗan – IG

Kasafin ƴan sanda na 2021 ya yi kaɗan – IG

152
0

Babban Sufetan yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu ya bayyana cewa horas da jami’an yan sanda na daga cikin abinda za su fi ba fifiko a kasafin kudin badi.

Muhammad Adamu ya bayyana hakan ne yayin da yake kare kasafin kudin rundunar na shekarar badi a gaban kwamitin harkokin yan sanda na majalisar dattawa.

Ya ce rundunar ƴan sanda karkashin jagorancinsa ta kudiri aniyar samar kyakkyawan yanayin tsaro sakamakon kalubalen da kasar ke fuskanta a fannin tsaro.

Ya kara da cewa Naira milyan dubu 11 da aka ware wa rundunar a kasafin kudin shekara mai kamawa yayi mata kadan matuka wajen samar da kayayyakin aiki, don haka yayi kira ga majalisar da ta kara masu kudi domin su samar da kayan aiki na zamani da za a horas da jami’ansu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply