Home Kasashen Ketare Kasar Bahrain: Zartar da hukuncin kisa ya janyo zazzafar muhawara

Kasar Bahrain: Zartar da hukuncin kisa ya janyo zazzafar muhawara

86
0

Daga Rahama Ibrahim Turare

 

Kasar Bahrain ta zartas da hukuncin kisa ga wadansu mutane 3 bisa kama su da aka yi da aikata laifuka daban-daban.

Laifukan dai sun hada da ta’addanci da kashe jami’in Dansanda da kuma kashe wani limamin masallaci, kamar yadda mai gabatar da kara ya gabatar.

Firaimistan Bahrain Hamad Al Khalifa

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama dai sun sha jan kunnen kasar ta Bahrain akan zartas da hukuncin kisa ga mutanen biyu.

Mutanen da aka zartas da hukuncin kisan kan su su ne Ali Muhammad Hakeem Al’arab da kuma Ahmad Isah Ahmad Almalali.

Kungiyoyin dai sun ce, yanke hukuncin kisa cin zarafi ne ga rayuwa da kuma azabtarwa.

A watan Janairun 2018 dai ne aka gurfanar da mutanen biyu gaban kuliya.

Mai bada rahoto na musamman majalisar dinkin duniya Mr. Agne Callamard ya ce Arab da Almalali sun rasa duk wata dama ta daukaka kara a ‘yan dakiku kadan kafin a kashe su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply