Home Kasashen Ketare Kasar Burundi: kusan rabin mutanen kasar  na dauke da cutar  maleriya

Kasar Burundi: kusan rabin mutanen kasar  na dauke da cutar  maleriya

84
0

Daga  Abdullahi Garba Jani

Rahotanni daga kasar Burundi, na cewa sama da mutane 1,800 ne cutar zazzabin maleriya ta kashe a kasar Burundi.

Rahoton hukumar kula da harkokin taimakon jama’a na majalisar dinkin duniya ya tabbatar da cewa a shekarar 2019 an samu bullar cutar zazzabin maleriya har milyan 5.7 a kasar ta Burundi, kusan rabin mutanen kasar.

A yawan wannan bullar cutar da aka samu, mutane 1,801 suka mutu ta dalilin cutuka masu nasaba da cizon sauro daga watan Janairu zuwa na Yuli na wannan shekarar.

Taswirar Kasar Burundi

Kasar Burundi dai na da yawan mutanen da ba su wuce milyan 11. Kasar na makwabtaka da kasar Burundi, wato kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo wadda take take fama da cutar Zazzabin Ebola da ta halaka mutane da dama.

Tun a shekarar 2015 kasar Burundi ke fama da rikice-rikice bayan da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya sake tsayawa takara a karo na 3 kuma ya lashe. Masu sharhi kuma na ganin cututtuka na yaduwa a sakamakon  rikice-rikicen saboda babu sukunin samun nagartacciyar kulawar likita.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply