Home Noma da Kiwo Kasashen Afrika na shigo da abinci na Dala bilyan 50 a duk...

Kasashen Afrika na shigo da abinci na Dala bilyan 50 a duk shekara- AFDB

81
0

Abdullahi Garba Jani/dkura

 

Bankin raya kasashen Afrika AFDB ya ce kasashen nahiyar Afrika na shigo da abinci na kudi Dalar Amirka kusan milyan 50 a duk shekara.

 

Wata takarda daga jami’in watsa labarai da hulda da jama’a na bankin, ta ce daraktar bunkasa walwalar jama’a ta bankin Jennifer Blanke ce ta fadi haka a gaban wani kwamiti a taron kasashen duniya karo na 7 a birnin Tokyo na kasar Japan.

Tambarin Bankin Raya Kasashen Afrika, AFDB

Mrs Blanke ta yi bayin cewa abin takaici ne ganin yadda har yanzu nahiyar Afrika ke shigo da abinci duk kuwa da kaso 60% na kasar noma da Allah Ya huwace ma ta a duniya.

 

Ta ce kasashen Afrika na iya samun gagarumin ci gaba idan shugabannin kasashen suka himmatu wajen noma amfanin gona.

 

Sai Mrs Blanke ta yi la’akarin cewa da tallafin cibiyoyi da hukumomi irinsu Bankin bunkasa nahiyar Afrika AFDB za a samu yi wa tufkar hanci.

 

Kazalika, ta yi korafin cewa duk da yawan mata manoma da ake da su a Afrika, amma har yanzu su ne jujin zuba shara musamman a aikin gona.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply