Home Labarai Kasawar Buhari na neman halaka Nijeriya – Secondus

Kasawar Buhari na neman halaka Nijeriya – Secondus

105
0

Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP Prince Uche Secondus ya ce ƴan Najeriya sun faɗa cikin mawuyacin hali saboda gazawar gwamnatin APC wadda shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta.

Secondus ya bayyana hakan ne ranar Laraba, a garin Bauchi, inda ya ke cewa gwamnatin ba ta nuna damuwa da halin da kasar ta shiga musamman a ɓangaren rashin tsaro.

Ya kuma kirayi shugaban kasar da ya ayyana dokar ta ɓaci a ɓangaren tsaron ƙasar.

Secondus ya kuma nuna damuwarsa kan halin da kasar nan ke ciki bisa kashe kashen da ke faruwa, ya kuma bukaci shugaban kasar da ya kwato daliban da aka sace, tare da yabawa gwamnan Bauchi kan kokarin da yake dan ganin ya inganta rayuwar mutanen jiharsa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply