DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeBabban Labari Kashi 61% na magidanta a Nijeriya na fama da matsanancin talauci –...

Kashi 61% na magidanta a Nijeriya na fama da matsanancin talauci – Rahoto

Binciken kungiyar Enhancing Financial Inclusion & Advancement (EFInA) ya bayyana cewa kashi 61 cikin 100 na manyan ’yan Nijeriya na cikin matsananciyar matsalar rashin wadatar kuɗaɗen gudanar da rayuwa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito rahoton Access to Financial Services in Nigeria (A2F) na shekarar 2026, wanda aka fitar a Abuja, ya nuna cewa duk da karuwar shigar ’yan Nijeriya cikin tsarin hada-hadar kuɗaɗe ta yanar gizo, hakan bai haifar da ingantacciyar hanyar samun kuɗi ga kowa ba.

Rahoton ya ce kashi 71.6 cikin 100 na mutanen da suka fuskanci matsalar tattalin arziki sun dogara da hanyoyin magance matsalar da za su iya ƙara raunana rayuwarsu, yayin da kashi 13.8 kacal suka yi amfani da hanyoyin da za su taimaka wajen kare ko inganta yanayin kuɗinsu.

Haka kuma, matsalar basussuka ta ƙaru, lamarin da ke nuna cewa samun damar yin amfani da hidimomin kuɗi ba lallai ne ya kasance daidai da samun ƙarfin tattalin arziki ba.

Kungiyar ta ce yawan mutanen da ba sa cikin tsarin hada-hadar kuɗi ya ragu zuwa kashi 21 cikin 100, amma matsalar ta fi yawa tsakanin masu ƙaramin ƙarfi.

Rahoton ya nuna cewa kashi 53 cikin 100 na mutanen da ke cikin rukuni mafi ƙarancin arziki har yanzu ba sa amfani da tsarin kuɗi na zamani, yayin da hakan ya shafi kashi ɗaya kacal na masu arziki.

Haka kuma, kusan rabin mutanen da aka ware daga tsarin kuɗin na cikin kaso 20 cikin 100 na mafi ƙarancin masu arziki.

Rahoton ya kuma nuna gagarumin sauyi wajen amfani da harkokin kuɗi na zamani, inda amfani da digital finance ya tashi daga kusan kashi 47 zuwa kashi 64 cikin 100.

Amfani da mobile money ma ya ninka fiye da sau uku, daga kashi 12 cikin 100 a shekarar 2023 zuwa kashi 38 cikin 100 a 2026.

Sai dai EFInA ta ce har yanzu bai kamata a dogara da tsarin dijital kaɗai ba, saboda akwai al’ummomi da dama da ke fuskantar matsalolin samun damar irin waɗannan hidimomi.

A ɓangaren tanadi kuwa, rahoton ya ce amfani da tsarin ajiya na kuɗi na hukuma ya ƙaru daga kashi 38 zuwa kashi 53 cikin 100, yayin da samun rancen kuɗi na hukuma ya tsaya a kashi 10, inshora kashi biyar, sannan tsarin fansho ya kai kusan kashi tara.

Shugabar EFInA, Foyinsolami Akinjayeju, ta ce rahoton ya kuma nuna ƙalubalen da mata, manoma, ’yan kasuwa da matasa ke fuskanta, inda kashi 51.2 cikin 100 na manoma suka fuskanci wata matsala ta tattalin arziki, sannan kashi 52.2 cikin 100 daga cikinsu suka yi amfani da hanyoyin da za su iya ƙara raunana arzikinsu.

A nasa jawabin, tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, ya yi gargaɗin cewa bai kamata Nijeriya ta riƙa watsi da manufofin tattalin arziki da suka haifar da ci gaba ba.

Sanusi ya ce ƙasar ta taɓa samun ci gaba wajen rage hauhawar farashi da ƙarfafa tsarin manufofin kuɗi, amma sauya waɗannan manufofi ya tilasta mata komawa baya tare da sake dawowa farko.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata