Home Labarai Kashi 80 na masu filaye a jihar Borno basu da shaidar mallaka

Kashi 80 na masu filaye a jihar Borno basu da shaidar mallaka

148
0

Gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa kashi 80 na kadarorin garin Maiduguri da kewayenta ba su da takardun izinin mallaka.

Shugaban hukumar ɗaukar bayanai na taswirar jihar Alhaji Bashir Shatima ne ya sanar da haka a yayin wani taron da ya yi da manema labarai a Maiduguri babban birnin jihar.

Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda akasarin waɗanda suka mallaki filaye, sun samu filayen ne ta hannun dillalai da kuma shugabannin mazaɓu shi ya sa ba su da takardar mallakar filayen.

Ya ƙara da cewa da yawa daga cikin al’ummar jihar na samun matsaloli wajen ciwo bashi a hannun gwamnati da ma Bankuna, sakamakon rashin shaidar takardar mallakar filaye.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply